September 24, 2020

ƳAR UWA KI TAMAKA MINI NA AURI MIJIN KI : Wasikar da wata Baiwar Allah ta aikewa wata da take so ta taimake ta

 

Banda aminiyata Aisha Haroon Kabeer
Wacce jarumar kuka sani datayi kokarin aikata hakan.?

 

ƳAR UWA KI TAMAKA MINI NA AURI MIJIN KI : (Wasikar da wata Baiwar Allah ta aikewa wata da take so ta taimake ta)

Gaisuwa da fatan alheri a gare ki. Nasan zaki yi mamakin ganin wannan wasika tawa, amma kada hakan ya baki mamaki duba da irin matsanancin halin dana samu kaina a ciki, sakamakon soyayyar Mijin ki da Allah ya jarrabe ni da ita.

Ƴar Uwa! Na haɗu da Mijin ki ne ta hanyar shafin sadad da Zumunci na Facebook, kuma mun haɗu ne kamar yadda sauran Abokai ke haɗuwa, na kamu da matsananciyar soyayyar Mijin ki ne sakamakon yadda yake tafiyar da rayuwar sa. Mijin ki ya kasance mutumin kirki, mai son Mutane tare da kyautata musu, Allah ya hore masa fikira da iya tsara magana, hakan yana burge sauran Mutane bani kaɗai ba, ganin gwanin iya kwalliya, duk irin kayan daya saka suna yi masa kyau sosai.

Bayan mun fara gaisawa dashi ta in box ne, sai na bukaci daya bani lambar sa, ya kuma bani, a haka muka fara gaisawa dashi. Idan kuwa ya saka sabon hoto a facebook bana yin wata wata wajen yin downloading, don yanzu haka ban san iya yawan hotunan sa da suke cikin waya ta ba.

Bayan da cutar son sa ta fara ɗimauta ni ne na yanke shawarar sanar dashi muradina. A take yace dani shi ma yana so na, amma Soyayya irin wadda Musulmi ke yiwa Ɗan Uwan sa Musulmi, domin shi bashi da niyyar kara aure, kuma baya so yayi soyayya babu aure sannan kuma baya so yayi aure babu soyayya. Da naji hakan maimakon na hakura, ai kawai sai na cigaba da nace masa, ni a gani na hakan zai sa ya waiwayo gare ni. Bayan nayi duk me yiwa domin ganin haka na ya cimma ruwa ne amma abin yaci tura, sai na fara bincike akan ki domin kila kulawar da kike bashi ce tahana shi ya karɓi muradina.

Bincike na ya tabbatar mini da hakan yayin da shi da kan sa yake faɗa mini cewa shi fa kin ishe shi, bashi da bukatar kara Mata.

Gashi dai ni bazan iya hakura da Mjin naki ba domin gani nake kamar idan ban aure shi ba to babu wani ɗa Namiji da zan iya aura. A da, ina daga cikin Matan da basa kaunar sharing ɗin Namiji da wata, amma a yanzu tunani na ya sauya. Ina ganin koda Mijin naki Mata uku gare shi to zan iya shiga a ta huɗu.

Yar Uwa! Ki taimake ni, ki shawo mini kan Mijin ki ya aure ni. Na yi miki alkawarin zaki same ni a matsayin Ƴar uwa ba Kishiya ba.

Ki ɗauka ke ce a matsayin da nake ciki. Ki taimake ni. Idan wannan wasika tawa ta ɓata miki rai, ki gafarce ni, ba laifina ba ne, zuciya ta ce ta janyo, kuma na kasa control ɗin ta.

Nagode.

Daga Mai son Mijin ki….

To fah! Ƴar Uwa idan kece aka turowa wannan wasika, wanne mataki zaki ɗauka??

 

Source: Gidan Marubuta Hausa

Kawai don Nishadi

Leave a Reply