Ɗaya Daga Cikin Matan Atiku Abubakar Ta Fice Daga Gidansa Saboda Auren Mata Ta 4 Da Yayi, Inji Jaridar Peoples Gazette

Rahotanni sun nuna cewa ƙarin auren da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar yayi da matarsa ta 4 wadda ƴar asalin ƙasar Morocco ce na neman kawo masa tarnaƙi a gida.
Jaridar Peoples Gazette ta ruwaito cewa matar Atiku ta 3, Jennifer Douglas Atiku ta fice daga gidansa inda ta koma birnin Landan da zama. Sai dai zuwa yanzu babu bayani akan cewa ko tana neman rabuwa da mijin nata ne ko kuwa a’a.
A shekarar 2017 ne dai Atiku ya auri matarsa ta 3 kuma a shekarar 2018 ne suka samu ƙaruwar ɗa namiji, kamar yanda majiyar ta ruwaito. Sai dai zuwan wannan mata baiwa Jennifer daɗi ba saboda irin kulawar da take samu daga Atikun ta ragu.
Wata majiyar iyalan gidan Atikun ta bayyanawa Peoples Gazette cewa lallai tafiyar Jennifer bata rasa nasaba da Auren da Atiku ya ƙara. Sai dai da Peoples Gazette ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Jennifer, ta ƙi cewa komai, haka ma kakakin Atiku ya ƙi cewa komai kan batun.
Wata majiya ta bayyanawa kafar cewa ana sa ran kamin 2023, Atikun zai yi ƙoƙarin warware wannan matsala saboda tana iya kawo masa matsala a son sake tsayawa takarar shugabancin Najeriya da yake son yi. Majiyar dai ta bayyana cewa, Atiku yayi ƙoƙarin ganin ɓoye wannan magana bata fito bainar duniya ba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author