Nanda Shekaru 32 APC Zata Cigaba Da Mulki A Najeriya-Maimala Buni

Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya na riko Mai Mala Buni ya bayyana cewar jam’iyyar na bukatar zama a kan karagar mulki na shekaru 32 domin fitar da kitse a wuta ta yadda Yan Najeriya zasu ci ribar dimokiradiyya.
 
Mai Mala Buni ya fadi hakan ne Yayin da yake kaddamar da kwamitin tintiba na Jam’iyyar Buni yace zasu inganta rayuwar Yan Najeriya muddin aka basu wannan damar na jagorancin kasar domin yin wa’adi 8.
 
Shugaban Jam’iyyar yace fatar su itace samar da hanyar da zai basu damar yin wa’adi na 6 da 7 da kuma 8 akan karagar mulki domin aiwatar da manufofin su wadanda zasu inganta rayuwar Yan Najeriya.
Buni wanda shine Gwamnan Jihar Yobe yace suna cigaba da samun nasara wajen janyo jiga jigan yan siyasa suna shiga jam’iyyar ta su, yayin da aka kuma baiwa ‘yayan jam’iyyar damar sabunta rajistar su domin cigaba da taka rawa a cikin ta.
 
Ko kuna fatar cigaban mulkin jamiyyar APC a Nijeriya nanda Shekaru 32 kamar yadda mai Mala Buni yake fada.......? muna dakon ra'ayoyin ku a shafinmu na Facebook wato

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author