2023: Na Tsaya Takara Ne Domin In Ceto Najeriya- Gwamna Yahaya Bello

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi,  ya fito fili ya bayyana burinsa na tsaya wa takarar Shugabancin  Nijeriya a shekara ta 2023 idan Allah mai ya kai mu lokacin, inda yace, yana da burin tsaya wa takarar ne, domin dawo da Nijeriya cikin hayyacin ta.

Gwamna Yahaya, wanda ya zanta da gidan Jaridar Daily Independent a ranar Lahadi 10/01/2021, ya tabbatar da cewa, ya shiga neman takarar ne, don magance dimbin matsalolin dake addabar kasar mu Najeriya, inda yayai kira ga ’yan Najeriya dasu mara masa baya gurin fafutukar dawo da kasar daga kalubale da take fuskanta yanzu.

 

“Ina so da kowa-kowa da ya hada hannu da ni, domin dawo da kasar nan daga halin-ko-’in kula da ta tsinci kanta a ciki. Ya zama dole mu kara yin amfani da wannan damar da muka samu gurin ganin mun kwato kasarmu daga halin da take ciki,” inji Gwamna Yahaya Bello.

“Da izzinin Allah, na shirye tsaf domin na shugabanci kasarmu Nijeriya kuma zan iya-iyawa ta na samar da shugabanci mai kyau a kasar nan.

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author