Babban mai magana da yawun, Injiniya Abba Kabir Yusif (Abba Gida-Gida) Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar da cewa idan Allah ya basu damar lashe zaben 2023 a jihar Kano zasu rushe gine-ginen da aka yi ba bisa ka'ida ba.
Bature Dawakin Tofa ya fadi hakane a dandalin sada zumunci na Facebook inda ya wallafa cewa, za suyi maganin “Wadanda suka lalata al’adu da kayan tarihi gami da tattalin Arziki”.
Kuma “Insha Allah, kwana dari na farko zai kasance ne na rushe dukkanin wani gini da aka gudanar da shi a guraren al'umma.
Sannan zamu “Sake Nada Sarki Sanusi tare da rushe Sarakun Kauye da mayar da Kano kasaitacciya Insha Allah”, cewar Bature Dawakin Tofa.
You must be logged in to post a comment.