A Cikin Kwana 1 Aliko Dangote Ya Yi Asarar Dala Miliyan 900

Shugaban kamfanin Dangote group Alhaji Aliko Dangote, yayi asarar Dala Miliyan 900 a hada-hadar kudaden hannun jari a Najeriya, kamar yadda gidan jaridar kasuwanci ta Bloomberg ta wallafa.

Bloomberg wadda tafi bayar da rahoto kan mutanen 500 waɗanda suka fi kowa kuɗi a fadin duniya, ta wallafa kuɗin attajirin Dangote sun ragu daga biliyan $18.4 a ranar Alhamis 07/01/2021 zuwa biliyan 17.5 a ranar Juma’a 08/01/2021, wanda hakan yasa ya sauko daga mutum na 106 zuwa na 114 a jerin masu kuɗin duniya, kamar yadda Punch ta wallafa.

A watan Disambar shekara ta 2020 ne jumullar kuɗaden Aliko Dangote ya kai dala biliyan 17.8 daga dala biliyan 15.5 da yake dasu a baya.

Dangoten dai ya sake samun ƙarin kudaden ne har dala miliyan 600 a farkon makon Janairun shekara ta 2021, sai dai kuma yayi mummunar asarar duka kuɗin a Juma’ar da ta gabata.

Duk da haka Dangote shi ne wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika, haka kuma shi ne ya fi kowane baƙar fata kuɗi a duniya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author