Abin Daya Kamata Ka sani Game da Karkarwar Hannu ga Mai Shanyewar ɓarin Jiki

Karkarwar hannu na daga cikin ƙalubalen da masu shanyewar ɓarin jiki kan fuskanta yayin warkewa, musamman idan matsalar ta ritsa da sashin tacewa da dai-daita motsi da ke ƙwaƙwalwa. Karkarwar hannu na kawo rawa, bauɗewa ko walkacewar hannu yayin ƙoƙarin gudanar da ayyukan yau da kullum kamar cin abinci ko abinsha, yin rubutu, sa hannu ko zane, yin kwalliya, rufe ko buɗe botirin riga da ma sauran ayyukan sana'a da ke buƙatar saiti sosai.
 
Misalin yadda mai shanyewar ɓarin jiki ke jin karkarwar hannu a jiki shi ne kamar a riƙa tankwaɓar hannunka yayin da kake ƙoƙarin kai hannu, cokali ko kofi bakinka ko kuma yayin rubutu ko zane.
 
A yayin da mai shanyewar ɓarin jiki yake cikin wannan matakin warkewa, likitan fisiyo na mayar da hankali wajen tsara hanyoyin rage karkarwar hannu har zuwa lokacin da mutum zai iya dukkan ayyukan yau da kullum ba tare da wannan matsala.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author