August 10, 2020

ABIN TAKAICI: Tsoho Mai Shekaru 60 ya yi wa yarinya yar shekara 8 fyade

ABIN TAKAICI: Tsoho Dan Mai Shekaru 60 ya yi wa yarinya yar shekara 8 fyade

Haruna Lawal

Kamar yadda majiya ta jiyo Mana cewa tsohon ya yiwa yarinya Mai tallar Kifi ne fyaden a wani kango.

Yan sandan jihar Niger sun samu damar kama tsohon Mai suna Haruna.

Bincike ya nuna cewa alamarin ya faru ne misalin da karfe 1:30 na ranar Asabar 11 ga watan Julin wannan shekara ta 2020 lokacin da yarinyar ke tallan Kifin nata.

Haruna Lawal ya yi amfani da damar na kai yarinyar wani Kangon Gini inda ya Bata kudi N100 daga nan kuma ya aikata mata fyade.

Haruna ya amsa laifinsa lokacin da yan sabda ke gudanar da bincikensu game da aukuwar lamarin. Za a gurfanar da Haruna Lawal Mai Shekaru 60 a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp: https://chat.whatsapp.com/FkwQ5aI1kcFGBg7zPKVR5A

Domin aiko labari, shawara a tuntubarmu ta sgl.newshub@gmail.com

SHAFIN MU NA SADA ZUMUNTA NA FACEBOOK

Facebook.com/sglnewshub

Instagram.com/sgl.newshub