AIYUKAN JINKAI

ALLAH YA TAIMAKE MAI TAIMAKO

Lahadi, 01/11/2020

 

A yau ne aka yaye mutane 100 tare da basu kayan da zasu fara sana'a a garuruwan *Yalango* (Masama) da *Naman Goma* (Maruda) 

 

Kungiyar *Shettima Foundation Gwandu* karkashin shugabancin *Hon (Dr) Usman Buhari Ali Gwandu* ta hada taron horarwa na kwana shida samar da sana'o'in yi da rage radadin zafin rayuwa ga al'ummar garuruwan bayan iftila'in barnar ruwa da ya faru a cikin karamar hukumar mulki ta Gwandu.

 

Samari 40, Mata 40, da Uwaye Mata 20 ne aka yiwa horon koyarwa akan sana'o'in hannu na yin faudan fuska, sabulun wanki, sabulun wanka, man shahi, turare, kayan goge-goge, da dai sauransu. 

 

Taron ya samu halartar jama'a daga garuruwan biyu da kuma masu kula da shirye-shiryen wanda suka hada da Kansiloli, Hakimmai da ma'aikatan gwamnati. 

 

Saura sun hada da Mukhtar Maruda (tsohon Kantoman karamar hukumar Gwandu), Umar Hassan (Dr Badadi), Alh Bilyaminu Aliyu 

(Shugaban Matasan Karamar Hukumar Gwandu), Alh Usman Ladan (Pro), Faruku Bala Gwandu Sconjor (Chairman, Gwandu Local Government Social Media & Publicity Forum, Faruku Modi Masama, Shamsu Abdullahi,  Faruku Maigujjiya Dodoru, da dai dauransu

 

Bayan kaddamar da bada talafin, Shattiman Garin Gwandu ya wuce wurin gabatar da ta'aziya ga iyalan marigayi *Mallam Mairogo Danbahu* wanda jagora ne a jam'iyyar APC a cikin mazabar *Maruda* mai kimanin shekaru 55 da Allah yayiwa rasuwa cikin garin *Naman Goma*.

 

  • Muna fatan da adduar Allah yaqara daukaka mana *Hon Usman Buhari Ali Gwandu* wanda babu ruwansa da nuna bambanchi adukkan ayyukan alkhairin dayake bijirowa dasu

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State