AKWYI LAUJE CIKIN NADI

Idan kana bibiyar zanga-zangar #ENDSARS zaka fahimci cewa sunada wata boyyayar manufa.

 

A yanzu danake wannan rubutun sunada kusan Naira miliyan 50 ta suke tarawa a tsakanin su, don siyan abinci, kuma har har yanzu basu daina karbar tallafi ba.

 

Acikin daren jiya CEO din Twitter yayi verifying accounts wadanda suke kan gaba a zanga-zangar yakuma bude musu sabowar hanyar da zasu karbi taimako ta hanyar bitcoin.

 

Ba ina kokarin kashewa masu shirin zanga-zanga a arewa gwiwa bane, amma ina ganin yakamata muyi tunanin abubuwa kamar haka.

 

1. Idan tunanin yan kudu shine kawo juyin juya hali a Nigeria, yin zanga-zanga a arewa bazai taimakawa kudrinsu ba?

 

2. Munsani hukumar yan sanda tana karkashin ikon gwamnati, hakan na nufin gwamnati zata iya sawa ko hanawa, haka kan boko haram da yan ta'adda? Idan ba haka bane, muna tunanin zanga-zanga ce, zatayi aiki?

 

Idan dan kudu yace #ENDSARSNOW gwamnati ta dau biro da soke SARS, hakane da banditry da kuma Boko Haram?

 

Tabbas idan borin yan kudu shine kawo juyin juya hali, to zanga-zangar yan arewa zata kara rikita Nigeria kawai, kuma hakan taimakon su.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State