Al'ajabi: Mutum Za Ka Mutu

Abun Al'ajabi: Mutum Za Ka Mutu!

 

Daga Mairo Muhammad Mudi

 

Jiya na ji wani labari da ya ba ni mamaki da mutum da irin tunaninsa!

An ce an yi wani mutum ne a daya daga cikin garuruwan Arewacin kasar nan kuma ya shahara a kan shi matsafine kuma boka inda ya ke alfahari da wannan sana'a tasa. 

 

Shi kadai ya san yadda ya yi nisa a harkarsa kila sai masu bibbiyarsa suna amfana da mugun aikinsa don irin kirarin da ya ke wa kansa cewa, ko da mahaifiyar sa ce ke da makullen Aljanna ya san ba za ta bude masa ya shiga ba! Subhanallah! 

Kuma a haka ya ci gaba da rayuwa inda aka ce ya tara dukiya da dama don kuwa ya gina gida na gani na fada! Ana nan ana nan sai watarana ciwon ajali ya kama shi, duk wanda ya zo kusa da shi don gaishe shi sai ya kama shi da cizo har sai ya bare fatan jikinsa. 

 

Da aka gane haka kuma babu yadda za a yi da shi, sai aka tura shi cikin daki aka kulle. Abincinta windo ake hurga masa don da ya ga gimawar mutum sai ya yi ta ihu Yana kokarin kamo shi don ya ciza. Aka rufe shi lif inda ba zai ga kowa ba, ba za a gan shi ba. Sai dai a yi Masa kwallo da abinci ta taga.

 

Za a ji yana ihu yana kururruwa. Bayan kwanaki kadan sai aka ji an kwana an wuni ba a ji muryarsa ba, sai a ka ce a duba, ana lekawa, sai aka gan shi kwance ya mutu amma babu kyau gani domin an ce duk jikinsa babu inda bai ciza ya ci ba. Hatta gabansa ya rabunda jikinsa! Aka shigo, aka tattara jikinsa aka saka a buhu, aka haka rami aka zuba!

 

Wa ya taba jin labarin mutanen da saboda da tsafi, suke yakushe ko cizon kansu kafin su mutu? Ni kam ba yau na fara ji ba, an ce wasu mata Kan rinka sa hannu a gabansu suna ja, suna kururruwa, wasu sun ce irin wadannan mata ne ke wanke gabansu suna ba mazajensu don su mallake su, subhanallah!

 

Akwai kuma wasu za su rinka fadan abubbuwan mugaye da suka aikata kafin rai ya yi halinsa.

 

Mena ke kokarin fada maku anan 'yanuwa? Abu guda ne, mu ji tsoron Allah da ranar mutuwanmu! Kowa fatansa ya gama da duniya lamin lafiya, amma duk wanda ya kasance kuntata wa wasu don dama da sheidan ya ba shi, tabbas ya san ba zai gushe ba sai ya gilbi abusa a hannunsa kafin ya je can. Da masu yin da wanda ake masu su gane cewa, akwai ranar kin dillanci! A duniya kenan wannan mutumin ya ga tasa, saura can! Ana duniyar, Ina ga gargadi ne gare mu, mu ji tsoron Allah mu gujewa wa tsafi da mugayen aiki!

 

A matsayin mu na Musulmi, muna da baiwa da Allah Ya yi mana, Kur'ani Mai Girma, waraka ne a gare mu, duk matsalar da kake da ita komai girmarta, ka dage da kama ayoyin Allah, ga biyan bukata,ka samun nutsuwa bugu da kari ga dimbin lada! Sannan in lokacin tashi ya zo a rabu da kai cikin salama kana hasken koshi, kana murmushi In Shaa Allah. 

 

Haba me aka yi aka yi tsafi ko boka wanda biyar bukatar ta kankanin lokaci ne! In ka tsaya ka roki Allah, za ka ga duk biyan bukata da zai baka mai alheri ce in kuma babu, zai hana ka sannan Ya ba ka kwanciyar hankali da natsuwa! 

Amma Boka zai ce zai ba ka wanda fa ba dole ba ne bukata ta biya sannan in ma bukatar ta biya ba ka sani ko akwai bala'i da ke tattare kan wanna bukata ba sai daga baya ka yi nadama. Sannan in ba ka yi sa'a ba, nadamar za ta kasance babu amfani!

 

Na taba jin labarin wani mutum da ya je ya samu boka ya ce masa yana son ya yi kudi, boka ya ce an gama, ya kawo kaza, ya kawo, boka ya ce ya kai kazar nan daki ya zuba mata hatsi, duk yawan hatsin da ta ci yawan shekaru da zai yi yana jin dadin kudinsa kenan kafin ya mutu. Mutum ya amince kuma ya dauki kaza, sai da ya tabbatar ya bar ta da yunwa kafin ya kulle ta a daki tare da hatsin da boka ya ba shi. Amma kaza gyameme ta ki cin ko guda, an buga an buga ta ki, a haka ta mutu da yunwa. Ya ruga wajen boka amma boka ya ce babu yadda zai yi sharadin kenen. Hankalin shi ya tashi, yana dawowa ya yi hatsari ya mutu!

 

Kun ga ni rashin yarda da hukunci Ubangiji, da zai yi hakuri, in Allah Ya nufa zai yi arziki zai yi ba sai ya tafi wajen boka ba. Yadda kuma Allah bai nufa zai yi arziki ba da zai ba shi kwanciyar hankali kuma tunda Allah Ya nufa zai bar duniya a ranar, da zai bar duniya da imaninsa! Amma ya bar duniya babu kwanciyar hankali kuma a matsayin mushriki! Subhanallah!

 

Mu ji tsoron Allah mun san duk bukatunmu in namu ne muka yi hakuri ba mu nema ta gurbatacciyar hanya ba, Allah zai ba mu su ta kyakkyawar hanya sannan Ya kuma ba mu lahira da su!

 

Ya Allah Ka sa mu fi karfin zukatanmu, mu yarda da hukuncinKa a kanmu. Allah Kar ka bar mu da dabararmu. Allah Ka shirye mu a hanya madaidaiciya, Amin.

 

Assalamu alaikum.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author