Alamomin Ciwon Siga Biyar Da Mutane Ke Wasarere Da Su.

Da zarar ka fara fuskantar waɗannan alamu, tuntuɓi likita domin duba siganka.

 
1. Yawan zuwa banɗaki domin fitsari akai-akai, musamman da daddare.
2. Kamuwa da cutukan hanyoyin fitsari akai-akai, daga cikin alamun cutar hanyoyin fitsari akwai jin ciwo ko zafi yayin fitsari, musamman ga mata ko kuma fitar fitsari ko ruwa mai launin da ba a saba gani ba.
 
3. Ramewa ba tare da yin atisaye ko bin wata hanyar rage ƙiba/teɓa ba. Ana yi wa ciwon siga take da "ga ƙoshi; ga kwanan yunwa" saboda akwai wadataccen siga a cikin jini, amma jiki ba zai iya sarrafa shi zuwa makamashi da zai bai wa jiki kuzari ba. A maimakon haka, jiki zai riƙa narka ajiyayyen kitse da ke jibge a sassan jiki domin samar da makamashin kuzari ga jiki.
 
4. Raguwar gani: raguwar gani ko ta'azzarar [matsalar] gani na iya zama sakamakon hauhawar siga a cikin jini wanda ka iya lahanta jijiyoyi da sauran sassan ido.
 
5. Matsananciyar kasala ko gajiya: kasala, ƙaranci ko raguwar ruwan jiki (saboda yawan fitsari akai-akai), tare da ciwon ƙoda duk na iya alaƙantuwa da ciwon siga.
 
 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author