August 10, 2020

Aljannu ne suka yanke Mazakutar Mijina – Cewar matar da ake zargi a Taraba

Matar da ake zargin cewar ta yanke azzakarin Mijinta mai suna Maimunatu ta shiga hannu, inda take tabbatarwa Jami’an tsaro cewar lallai-lallai ita bata aikata abin da ake zargin ta dashi ba. Matar ta tabbatarwa  hukuma cewa aljannunta ne suka aikata wannan ta’adi, ita bata da masanar lamarin da ya faro.

Wasu daga cikin makotan ta sun tabbatar cewa kishi ne ya ingizata da ta aikata irin wannan aika aikan, saboda dama akwai rade-radin cewar bada jimawa ba mijin nata zai kara aure, a dalilin hakan yasa ta yanke masa mazakuta kowa ya huta.

zaku iya sauraren cikakken rahotun

Danna Nan Domin Kallon Video