An Damke Wani Dan Hakika A Jihar Yobe Don Batanci Ga Mahalicci Da Manzo

Jami'an tsaro a jihar Yobe sun cafke wani dan darika mai akidar HAKIKA sanadiyyar batunci ga Allah Madaukakin Sarki da Manzon Allah mai tsira da aminci. Dan Hakikan mai suna Kabiru ya yi munanan kalaman a taron maulidi a garin Damagum.
 
Lamarin ya jawo matukar husata daga jama'ar gari da su ke nuna gangancin ya kai daukar kowane mataki mai tsanani.
 
Shugaban kungiyar rundunar adalci na arewa maso gabar Alh. Zakare Adamu ya bukaci jami'an tsaro su dau tsauraran matakan dakile sake samun irin wannan akasi don za a iya samun keta doka da oda don jama'a ba za su lamunci irin wannan mummunar akida ba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author