An Kama mutane 200 da suka karya Dokar Kin Sanya Takunkumin rufe hanci (face mask) A jahar kano

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Gwawmnatin jahar Kano, ta Kama sama da mutum 200, da suka karya Dokar yaki da cutar Coruna, na Kin Sanya Takunkumin Rufe hanci "face mask"
....Tun bayan da Gwawmnatin ta Ayyana Dokar yaki da annobar Coruna, jami'an Tsaro ke tsare mutane a hanya domin zakulo wadanda basa Sanya Takunkumin inda za'a ci Tarar sure naira dubu biyar, Koh zaman Gidan yari na wata 6,.
Bayan da Dokar ta fara aiki a jahar kano, jami'an Tsaro sunyi nasarar cafke mutane 200, inda akaci tarar mutane 125, mutane Kuma guda 25 aka aike dasu Gidan Gyaran hali.
Hakan Yana kunshe ne cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai Mai Dauke da sahannun kwamishinan yada labarai, malam Muhammad Garba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author