An kori Rahama Sadau daga masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood.

Hukumar Masana’antar Kanywood ta sanar da korar jaruma Rahama Sadau daga masana’anyar Kanywood biyo bayan hotunan tsiraici da ta wallafa wadanda suka janyo cece-kuce har kuma takai ga cewar wani zindikin arne yayi batanci ga manzon Allah (S.A.W) akan hoton.

Tun a jiya ake ta samun martani iri-iri daga fannoni da dama gameda abinda jarumar tayi. Masu ruwa da tsaki a harkar Kanywood Irinsu Aminu S. Bono da Lawal Ahmad duk sun fitar da bidiyoyin Allah wadai akan abin da jarumar tayi.

To sai dai a safiyar yau Rahama Sadau ta saki wani sabon bidiyo mai tsahon minti 3 wanda acikin sa take kuka nata kuma bayyana na damar ta. Abinda yasanya dayawan mutane ke yaba mata.

Wannan dai ba shine karon farko da jarumar ke jawo irin wannan cece-kuce ba. Ko a baya an dakatar da jarumar sakamakon wani bidiyon waka da ya nuna tana rungumar wani mawaki mai suna classique.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments
jamilu - Nov 6, 2020, 10:20 AM - Add Reply

To

You must be logged in to post a comment.

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author