Ke Duniyar nan Ina Zaki Damu Ne: An Rataye Limami A Jihar Kebbi

Abubakar Zaki  Tari an sami gawarsa rataye a cikin kemis da ke kofar gidansa, akan titin masu sayar da tumatur bayan kara da ke cikin garin birnin kebbi a ranar 9 ga watan, Aprilun 2021 da dare.

Wata majiya ta kusa da iyalin marigayin ta bayyana cewa marigayin wanda aka fi sani da Dr Tari, ma'aikacin tiyata ne da ke Asibitin Gwamnatin Tarayya ta Federal medical center (FMC) a Birnin kebbi, wanda Kuma yana daga cikin Kwararrun sashen tiyata da ake ji dasu a Asibitin FMC na Birnin kebbi.

20210401_161208.jpg
 
Wani dan uwan marigayin mai suna Aliyu Umar, ya bayyana cewa " Mahaifiyar marigayin ta je gida ta same ni a gurin barci na da safe, ta sanar da ni cewa inje in nemo mata Alhaji a Masallaci gurin da yake bayar da Sallah, domin an neme shi ba a gan shi ba.
 
Haka aka yi na tashi na nufi Masallaci nayi tambaya a inda yake bayar da Sallah, wani ya gayamin cewa shima ya makara gurin zuwa Masallaci bai san wanda ya bayar da Sallah ba. Sai aka kira min Naibin Limamin Masallacin wanda ya shaida min cewa shi ne ya bayar da Sallah saboda Liman Alhaji Abubakar Tari bai zo ba.
20210401_161239.jpg
 
Sai kawai na dawo gida na fada masu cewa naje Masallaci baya can. Sannan sai na gan Kemist din inda yake aiki an bar kofa a bude. na je na leka, kawai sai na gan shi a rataye, Sai na ruga na a gigice na bugi kofar gidan makwabcinsa wanda yake a rufe,  sai kofar ta bude. Sai na fada mashi abinda na gani. Sai muka ruga, da ni da makwabcinsa da matarshi daya muka zo gurin.
 
Hmmmm abin da na sani kenan, daga nan ne na bar makwabcinsa tare da matarshi guda suna kururuwa, Cikin rudani da gigicewa na tafi gidan Malam Usman shi ma na gayamar,  Ko da na dawo na sami jama'ar unguwa sun yi yawa a wajen. 
20210401_161248.jpg
 
Alhaji makwabcin marigayin, a lokacin da na Kira shi, shi ma ya sa rigarsa ya je gurin ya leka ya ga marigayi a rataye da igiya, sai da ya fadi saboda tsananin kaduwa da gigita ! ".
 
Shi ko Malam Aliyu Umar, ya bayyana cewa marigayin Alhaji Abubakar Zaki dan asalin garin Tari a karamar hukumar Gwandu ne, kuma Limami ne, ga shi Malami mai wa'azi, sannan kuma gwani a harkar tiyatar fida a Asibitin (FMC) Birnin kebbi, ga shi da kokarin sannan hazakar da ya ke da ita ta sa shi yayi fice a wannan fanni, ya zauna lafiya da kowa, makwabta, wajen aiki, hulda da muamala mai kyau.
20210401_161216.jpg
 
Mutum wanda ke son dogaro da kansa ta hanyar yin sana'a komai kankantarta bayan aikin gwamnati. Ya rasu ya bar mata biyu da yara 7 maza 9 mata.
 
Lamarin da ya haifar da fargaba da dar-dar a tsakanin al'ummar  garin Birnin kebbi, tare da rokon Allah ya tona asirin wadanda suka yi masa wannan danyen aiki, a cewar wani abokinsa da yake kofar gidan marigayin tare da jama'a da ke kofar gidan don amsar gaisuwa da tausayawa.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author