An Sace Jami’ar Yaɗa Labarun Hukumar Shige Da Fice

Masu garkuwa sun yi awon gaba da jami’a mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasa, reshen jihar Edo, Bridget Esene, wani jami’in hukumar ya bayyana cewa an sace Mrs Esene ne ranar Lahadi a kan hanyarta ta zuwa coci.
An bayyana cewa ‘yan bindigar sun ta bibiyar jami’ar ne Esene har zuwa yankin Igueniro, dake babban birnin jihar, inda suka fitar da ita daga motarta suka jefa ta a motarsu.
Sha'anin satar mutane da yin garkuwa da su domin amsar kuɗin fansa na cigaba da zama wani babban kalubale a Najeriya, inda a kusan kowane lokaci masu aikata garkuwa ke Farautar mutane su nemi kuɗin fansa.
Duk da ƙoƙarin da gwamnatoci ke yi a kasar da jami'an tsaro za'a iya cewar kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu ta la'akari da yadda al'amurra ke ƙara lalacewa a kusan kullum.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author