An sami tashin gobara kimanin goma sha hudu a jihar Kebbi cikin mako daya-Dododo

Shugaban hukumar bayarda agajin gaggawa na jiahar Dokta Alhaji Sani Dododo ne ya bayyana haka lokacin da ya ke magana da manema labarai a garin Birnin Kebbi karshen makon da ya gabata.

Dokta Sani Dododo ya ce an sami tashin gobara har fiye da goma sha uku a kasa ga mako daya sai dai daga ciki gobara daya a garin Jega da kuma guda biyu a garin Argungu su ne suka fi babban muni inda wutar ta lakume manya-manyan gidaje ba tare da an cire  komai ba.

Sannan yayi kira ga al’umma musamman magidanta da su dauki matakan kare duk abin da ke kawo tashin gobarar, kuma magidanta musamman mazauna karkara su inganta wajen ajiye harawar su, domin sune  abubuwan da ke saurin kama wuta, don haka suma mazauna birane wadanda  anan ne aka fi samun hatsarin wutar lantarki da su tabbatarda sun kashe abubuwan kayan wutar lantarki idan sun gama amfani da su, idan kuma za a fita a kashe wutar gida gabadaya, don haka duk lokacin da wutar lantarki ta sami wata matsala kuma a nemo masana harkar lantarki.

 

Dakta Alhaji Dododo Ya cigaba da cewa wannan hukumar ta bayarda agajin gaggawa tare da hadin gwiwar hukumar kashe gobara ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tunatarwa da wayarda kan al’umma dangane da hatsarin wannan lokacin na sanyi ba wanda shi ne lokacin da mutane suka fi ma’amala da wuta musamman a mazauna karkara inda ya ce yanzu haka wannan hukumar tana nan tana nemo hanyar wayarda kan al’umma ta hanyoyin kafofin yada labarai da wasannin kwaikwayo.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author