An sayar da wata Tantabara akan naira miliyan 893.

Abin al'ajabi baya karewa  Mutumin da ya samu nasarar sayen tantabarar da aka yi gwanjon ta Champion Racer Armando, ana masa lakabi da "Lewis Hamilton na tantabaru".

 

BBC ta ruwaito cewa "Mutumin ya kasance yana kiwon tsuntsaye kala-kala da ya ke mai sha'awar kiwon ne.

 

"Tantabarar wato New Kim, maii kimanin shekaru biyu ta samu nasarar samun lambobin yabo da dama a wasu gasa da aka yi a 2018.

 

Yawancin tantarabarun da ke shiga gasar tsere na da farin jini kuma za su iya hayayyafa har zuwa tsawon wani lokaci, kuma ana kyautata tsammanin mutumin da ya saye ta zai yi amfani da ita ne wajen sama masa ƙwai.

 

Wadanda suka sanya gwanjon tattabarar sun ce wannan gwanjo ba a taba samun irinsa ba.

 

Sun ce farashin da aka sayi tattabarar ne ya kara armashin gwanjon da aka yi kuma abin mamaki ne ace an sayi tantabara mace a kan wannan tsabar kudi.

Source: BBC.

 

Bayanai sun nuna cewa akwai tattabaru da dama a Belgium kuma a wasu lokuta a akan yi amfani da su wajen samun ƙwai don a samar da irinsu da dama.

 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author