Ana Neman Cinye Arewa Da Yaki-Kungiyar Matasa

Mu sani cewa abinda yake faruwa a Arewa na ta'addancin Boko Haram, Garkuwa da mutane, harin 'yan bindiga duka wannan salo ne na yaki a zamanance, ana yakar nahiyar Arewan Nigeria da abinda ake kira "covert and overt operations", ta yanda wadanda ake yakar ba za su ankara da wa ke yakar su ba

 

Sabon salon yaki ne ake mana, manufar ita ce a yaki Arewa wajen karya mata tattalin arziki da neman ilmi, a ruguza mata tsarin tsaro, a kakaba mata talauci da rashin zaman lafiya, a yayata barna da kuma yawaita mutuwa cikin al'ummah, ta yadda mutane za su kasance kowa ta kansa yake

 

Sannan kuma a tabbatar da cewa lalatattun mutane cikin Arewa sune za'a basu damar zama  shugabanni a Gwamnati, Malaman Addini a mayar da su 'yan barandan gwamnati, masu fadin gaskiya kuma a kassara su

 

A hana noma da kiwo wajen tabbatar da rashin tsaro a Arewa, a yada makamai ko ina, a kona  kasuwanni lokaci zuwa lokaci, a hana karatu da wanzuwar ilimi a Arewa, a mayar da mutane 'yan gudun hijira, a mayar da matasan Arewa 'yan ta'adda, 'yan mata a dora su a hanyar  lalata da karuwanci

 

Wannan shine abinda makiyan mu suke shiryawa a kan Arewa, gaba daya sai nahiyar Arewa ta koma nakasassa, mutanen ciki  su zamanto bayi, a mulki 'yan Arewa mulkin zalunci ba tare da 'yanci ba

 

Ba zamu lura ba Manyan Kasuwannin jihohin Arewa suna cin wuta, ina sakamakon bincike akan tashin wutar kasuwannin Arewa? su wa ke sa maja wuta a manyan kasuwanni?  abin nufi tattalin arzikin Arewa ake neman ruguza wa?

 

Suna neman shafe ruhin fulani makiyaya ta hanyar yada batanci ga makiyaya a manyan kafofin watsa labarai don a hana kiwon shanu gaba daya, domin a raunata tattalin arzikin Arewa

 

Anki daukar mataki Kidnappers suna ta kama mutane ana talauta 'yan Arewa saboda biyan kudin fansa, mutane suna sayar da gidajensu da kadarorinsu da duk abinda suka mallaka wajen biyan kudin fansa, tactically 'yan Arewa ke biyan kudin da barayi ke sayan makami ana kashe 'yan Arewan

 

An tilasta mutanen kauyuka da suke noma yin gudun hijira don a hana noma gaba daya, a jefa rayuwar 'yan Arewa cikin yunwa da tsadar rayuwa

 

Ya kamata 'yan Arewa mu fahimta, mu samar wa kan mu da mafita kafin a cinyemu da yaki, idan akayi kuskuren zaben miyagun shugabanni a 2023 tabbas za'a shiga uku a Arewa,  Allah Ya kiyaye

 

Muna rokon Allah Ya jikan Arewa, Ya tausayawa Arewa Ya kawo wa Arewa sauki da mafita 

Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author