AREWAWA/HAUSAWA

AREWAWA/HAUSAWA MASU ABIN MAMAKI.

 

Ka duba Ka ga yadda suke shirye-shiryen ɓallewa da sunan kafa jami'an tsaron yankin gabashin ƙasar nan, amma a zahiri suna wannan shiri ne don ɓallewa daga taraiyyar Nijeriya wadda aka haɗa a cikin shekarar (1914) a zamanin mulkin Turawan Ingila. Na yi wa wannan ƙasidar  tawa  take ne da AREWAWA/HAUSAWA ne, don irin yadda yake ɗaukar abu da wasa ko kuma ya ga cewa abun ba zai yiyu ba, sai mu yi waiwaye adon tafiya; tun bayan samun ƴanci ake ta raɗeraɗn juyin mulkin aka wa Gwamnatin hadin Kan ƙasa a wancan lokacin, wadda Ndamdi Azikiwi ke jagoranta. Masana tarihi sun ce an sanar wa da mahukunta cewa ga Irin Kitimurmurar da Inyamurai/Igbo ke shiryawa, suna da kudurin yin juyin mulki Sannan su karkashe duk manyan Sojojin da ba na yankinsu ba, su Kuma yashe arzikin yankinmu, su mai da Yankin (Niger Delta) mai arzikin man fetur a Karkashin Haramtaciyar Kasar su ta Biafara, Kuma duk waɗannan tsare-tsaren nasu babu Wanda ba bai yi Nasara ba, Sai dai an samu akasi na rashin abinci da jiragen yaƙi da sojojin ruwa da na sama, shi ya sa aka iya cin su da yaƙi.

 

  1. To waɗanda ke da wannan tabon da manufofin Tunda kowa ya San Haka wannan Kabilar ta su take Kamar Yahudawa suna da tsare-tsare da maƙalƙalewa a kan kudurinsu, su ne za a Bari su kafa wata Runduna da sunan Rundunar tsaron yanki, Bayan an jiyo wata Hira da shi Wannan mazi Nnamdi Kanu din ya yi a Gidan Radiyonsa na Yanar Gizo Yana cewa a lalata dukiyar Yan Najeriya makiyansu, har ya bude layin Kira ana Kira ana fada masa Irin barnar da aka yi a yankuna daban-daban na Jahohin Yarbawa, Yana jin dadi Har suke rokon sa da ya Ba su Bindigogi Shi kuwa gogan ya ce kafin a ba su Bindiga ko lauje ko wuka ce a wajan kashe maƙiyinka ɗan Nigeria har ya Umarce su da cewa duk Mai so a Ba shi Bindiga, to ya koma can kauyensu ya Shiga Rundunar Sojojin Sa-kai ta Biafara, A lokacin da na ji Haka a Wannan hirar sai na yi Zaton Irin Farfaganda ce kawai yake yi Ashe da Gaske ne sai ga shi A Yan satuttukan da Suka gabata ya yi bikin Yaye Sojojinsu na Sa-kai na Biafara da suke Kira (Eastern Security Network) a fakaice, wannan Sansanin da suka haska a Yanar Gizo sun ce shi ne Sansani na daya akwai na biyu, duk da yake yana da wuya a iya Gane Gaskiyar Maganar, Amma dai koma mene ne ya kamata AREWAWA/ HAUSAWA su tashi tsaye. A nan Ina nufin duk wani ɗan Arewa walau Muslimi ne ko Kirista ko ɗan Gargajiya, Saboda muddin Aka Bari suka cim ma burinsu, to fa mu ma za mu ɗanɗana kuɗar mu.

 

 

Abin takai ci duk da fitowar Wannan Mumunar Manufar tasu da ta fito fili, Kuma suka Fara Kaddamar da ita tun a Zanga-zangar (Endsars), Sai Malam Bahaushe ya ce ma ai Ba su iya yin komai Karya suke, shi a nashi Zaton hakan ba zai taba yiyuwa ba, kamar dai yadda aka yi wannan Tunanin tun a wuraren 1962, haka yanzu ma Tunanin bai canja ba, kamar dai ya manta da Abin da ya afku a cikin yakin Basasar Kwanton baunar da aka yi wa Sojojin Nigeria a Abagana da Irin Asarar Sojojin da aka yi. Tarihi ya nuna Sojoji kusan Dubu 6000 aka rasa a wannan Kwanton baunar, Kuma Tarihi ya nuna Akasarin makaman da Sojojin Biafaran suka yi amfani da su a kwanton ɓaunar duk Kirar su ne Kama daga gurneti har Makamai masu linzami da Tankokin Yaki da Bindigogi, a lokacin da A Arewa Babu wani Kayan Yaki da ake kerawa, Irin waƴanda za a bari har su bude Sansanoni Horar da Sojojinsu su horara da su Kuma su Basu Makamai, to me ya yi Saura ❓ Amma duk da hakan Bahaushe sai ya ce maka ai komai Ba su iyawa. Ina Kira ga AREWAWA su mai da hankalin su su Kuma cire Bambancin Akida ko a Addini a gudu tare a tsira tare.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State