Auren Dan Kwankwasiyya Da 'Yar Kwankwasiyya Na Kara Samun Goyon Bayan Manya

Daga: Salisu Magaji Fandalla'fih

Kamar yadda kukaji soyayya ta kullu tsakanin, Nazeer Dan Autan Kwankwasiyya da Nanan Kwankwasiyya, da suka hadu a gidan madugun darikar Kwankwasiyya Sanata Rabi'u Kwankwaso wanda har magana tayi nisa.

Har takai ga Dan majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso a zauran dokokin majalissar jihar kano, Hon Mudassir Zawaciki ya dauki nauyin kayan dakin Amarya.

Yanzu haka kuma soyayyar na samun goyon bayan wasu manya-manya a cikin kungiyar darikar Kwankwasiyya irinsu, babban mai gidansa Alhaji Auwalu Mamman shima ya dauki alkawarin nauyin Auren ko nawa zaa Kashe daga Miliyan 1 zuwa kasa.

Sannan shima wani babban jigo a kungiyar ta Kwankwasiyyar wato Hon Idris Dankawu shi kuma ya dauki nauyin Sadaki.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author