Ba dukan Yan Bindiga bane Mutanen banza – Gwamnan Zamfara
Kamar yadda rahoton Legit Hausa Ya nuna Bello Matawalle, Gwamnan Jihar Zamfara, ya ce ba duka tsagerun ‘Yan Bindiga ba ne mutanen banza, wasu daga cikin su dole ce ta sa suka fadawa sana’ar.
Matawalle ya bayyana hakan ne ga manema labarai bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 18 ga Faburairu, 2021, Vanguard ta ruwaito Ya yi bayanin cewa yawancin yan bindigan sun shiga harkar ne saboda irin rashin adalcin da al'ummar gari ke musu. "Ba duk kansu bane mutanen banza. Idan ka bincike abin da ke faruwa, da kuma abin da ya sa suka dauki doka a hannunsu, wasu daga cikin su sun fuskanci zalunci ne daga wajen yan banga," Matawalle ya ce. " ‘Yan Bangan kan kai musu hari a rugarsu, su lalata musu dukiya kuma su kwashe musu dabbobi. Babu wanda zasu kai wa kara, shi yasa wani lokaci suke daukan fansa."
"Wasun su na zama a k’auyuka kusa ga gari. Duk lokacin da Sojoji suka kai hari, su kan lalata musu dukiya da dabbobi. Suna jin haushin wadan nan abubuwa. Idan ka tattauna da su, za ka gane hakan."
Source: Legit.ng
You must be logged in to post a comment.