September 19, 2020

Ba gaskiya bane batun bada bashi karkashin kungiyar Izala – Dr. Bashir

Ba gaskiya bane batun bada bashi karkashin kungiyar Izala – Dr. Bashir

Rahotun da Umar Mikail ya fitar a yau a shafin BBC Hausa shine Saƙon da ake yaɗa wa manhajar WhatsApp da bai bayyana adadin kuɗin da za a bai wa mutane ba a matsayin bashi daga gwamnatin tarayya
Kamar yadda saƙon da ake yaɗawa ta dandalin WhatsApp ya buƙaci mutane su yi rajistar neman bashin kuɗi daga Gwamnatin Tarayyar Najeriya.
BBC ta ruwaito cewa “Saƙon ya yi ikirarin cewa za a bayar da bashin ne ta hanyar ƙungiyar addinin Musulunci ta Izala tare da sahalewar Shiekh Dakta Bashir Aliyu Umar, Babban Limamin Masallacin Al-Furqan da ke Jihar Kano”.

Kamar yadda aka rubuta a saƙon:

“Ku yi kokari kuyi apply loan ne da gwamnatin najeriya zata bayar karkashin kuniyar IZALA. Sannan ku turawa yan uwa musulmai link din www.manaraabp.com.”
Saƙon ya ci gaba da cewa: “Wannan shine kadai ingantaccen Link din saboda haka idan aka samu wani sabanin wannan to kada ayi amfani dashi. kuma ya samu sahalewa ne daga Babban Malami DR. BASHIR ALIYU UMAR (ALFURQAN).”

Mene ne gaskiyar Lamarin?

Shehin Malami Dr. Bashir Aliyu ya musanta cewa wannan bayani ba daga wurinsa ya fito ba a cikin wani saƙo da ya wallafa a shaifinsa na Facebook, Malam yana cewa “Duk wata sanarwa daga wurina za a same ta ne kawai ta sahihiyar kafa ko kuma wannan shafin na Facebook . (https://www.facebook.com/drbaumar)
Ya cigaba da cewa “Ƴan uwa Musulmi wannan rubutu mai haɗe da link http://www.manaraabp.com a kan bashi na Manara ba ni da alaƙa da shi, don haka a guji yaɗa duk wata jita-jita mai alaƙa da wannan da sunana,” cewar Dr. Bashir.

KARANTA CIKAKKEN BAYANI AKAI TA WANNAN SHAFI
https://www.facebook.com/drbaumar/posts/1616431875184656

Farfesa Salisu Shehu na Jami’ar Bayero ta Kano ya wallafa hotunan wani taron wayar da kai da suka gudanar a Jihar Kano game da yadda za a nemi bashin Babban Bankin Tarayya CBN wanda babu ruwa a ciki.

KARANTA CIKAKKEN BAYANI AKAI TA WANNAN SHAFI
https://www.facebook.com/permalink.php?story_fbid=2765454713724256&id=100007792628835

BINCIKEN DA BBC TA GUDANAR YA GANO CEWA SAƘO DA AKE YAƊAWA BA NA GASKIYA BA NE, wasu ne ke yaɗa shi domin cimma wata buƙatarsu ta musamman.

Idan aka lura da saƙon, za a fahimci cewa akwai kura-kurai da yawa game da yadda aka rubuta shi – an karya ƙa’idojin rubutu masu yawa a ciki, hakan na nuna cewa ba masu ilimi ne sosai suka rubuta shi ba.

Shi kansa shafin http://www.manaraabp.com da aka ce ta nan ne za a nemi bashin, ba ya aiki yadda ya kamata. Misali babu bayanan masu shafin da za ku iya tuntuɓarsu idan kuna neman ƙarin bayani.
Kazalika form ɗin da za a cike ɗin bai bayar da damar saka wasu muhimman bayanai ba game da muradin da mutum yake so ya cimma idan an ba shi bashin, wanda dole ne a yi bayani idan har bashin sahihi ne.
Haka kuma babu gurbin da mutum zai cike adadin kuɗin da zai iya nema, abin da ya saɓa da abin da aka saba gani.
Hasali ma sun fi ƙarfafa neman bayanan mutum na sirri irinsu lambar BVN ɗin mutum da ta matarsa ko mijinta da kuma ta magajinsa wato next of kin – lambar BVN uku kenan suke nema.
Hakan yana nuna cewa sun fi damuwa ne da su samu bayanan fiye da buƙatar wanda ya je neman bashin, kuma za a iya amfani da bayanan domin a zambaci masu su.

Binciki asalin labarin

Shafukan sada zumunta na karya kan yi kokarin bayyana kansu a matsayin cewa sun fito ne daga manyan kafofin watsa labarai, a don haka ka duba shafi sosai kafin ka watsa bayanan da suka wallafa.
Shafukan da aka tabbatar da halaccinsu suna dauke da alamar shudi a Facebook, da Twitter da kuma Instagram.

Duk da cewa wannan wani lokaci ba zai gamsar ba amma yana da kyau a duba abin da wasu kafofin watsa labarai masu inganci ke cewa kan labari domin tabbatar da gaskiyar batu.

Tambayi kanka, shin ingantattun kafafan yada labarai na bada rahoton wannan labarin?

Hanyoyin bincika labari
Akwai hanyoyi da dama da za su taimaka maka wurin tabbatar da sahihancin hoto ko bidiyo. Google, da Bing da kuma Tin Eye duk suna duba asalin hoto, wanda kan iya gaya maka inda aka dauki hoto da kuma asalinsa.
Tabbatar da bidiyo ya fi wahala amma shafuka kamar InVid na bada damar gano inda aka yi amfani da bidiyon da aka wallafa a Facebook da YouTube a baya.

Duba asalin abin
Idan kana da ainahin hoton ko bidiyo, za ka iya samun bayanai masu muhimmanci game da su, ciki har da wuri da kuma lokacin da aka dauka da kuma na’urar da aka yi amfani da ita.
Abin takaicin shi ne da zarar an wallafa hotuna a shafukan sada zumunta to bayanansu na sali sai su bace.

Yi tunani kafin ka wallafa
Dole a yi taka-tsan-tsan saboda ka da a kara jefa mutane cikin rudani.
Kafin ka wallafa, ka tambayi kanka ko bayanan da ka ke da su sun inganta kuma ya karfin sahihancinsu yake.

Source: BBC Hausa
https://www.bbc.com/hausa/labarai-53714144