Ba Mu Karbi Gudummawar Kudin Korona Kota Sisi Ba-Minista Sadiya

Ministar Agaji, Jinkai da Inganta rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouk tace ma'aikatar ta bata amshi gudummawa kota sisin Kobo ba, anan cikin gida da kuma kasashen waje da sunan tallafin korona ba.

Minista Sadiya ta bayyana hakan ne a lokacin da take kare kasafin ma'aikatar ta na shekarar 2021, a gaban kwamitin Majalissar tarayya.

Ministar tayi wannan ikirarin ne bayan Najeriya ta karbi Bilyoyin kudade a matsayin kudaden gudummawar tallafin da yaki da cutar korona, daga hannun kamfanoni, bankuna da daidaikun jama'a.

Hajiya Sadiya Umar tace ko sisin Kobo ba abaiwa ma'aikatar ta ba acikin kudaden da wadanda wasu daidaikun jama'a da kamfanoni suka bayar da gudummawa ba.

Ya zuwa karshen watan Afrilu, kudaden da Najeriya ta tara daga gudummawa , sun kai naira Biliyan 27.160, tace amma ba abaiwa ma'aikatar ta ko sisi ba.

Wasu da suka bada gudummawa mai tsoka sun hada da Aliko Dangote, Abdulsamad Rabi'u, Segun Agbaje (GTB), Tony Elumelu (UBA), Oga Otudeko (First Bank), Jim Ovia (Zenith Bank) Herbert Wigwe (Access bank) da kuma Femi Otadola (APD).

Da take magana akan rabon tallafi , cewa tayi ma'aikatar ta abinci kawai ta karba daga hannun gwamnatin tarayya.

"Ba mu karbi ko sisin Kobo ba, amma mun karbi kayan abinci," inji Minista Sadiya.

Ta kara da cewa baya ga kasafin ma'aikatar, ba su karbi karin kudi ko naira daya ba daga hannun gwamnatin tarayya da sunan kudaden tallafin raba wa jama'a ba.

Hajiya Sadiya ta bayyana cewa daga cikin kasafin ma'aikatar, kashi 50 kadai ta iya karba daga hannun gwamnatin tarayya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author