BA MUNAFURCI NE

NI ƊAN AREWA NE, KUMA BAHAUSHE

 

Abin zai matuƙar baka mamaki idan ka riski wani yana ta ɓaɓatu da hayagagar kiran al'ummar yankin Arewa da munafukai. Ko dan, nayi wannan batun a baya. Dan haka bari na ɗora!

 

Ba munafukai muke ba, ba kuma kidahumai bane ballantana mu zamanto lusarai don kawai ba muyi koyi da maƙwabtanmu ba.

 

Hakan kuma baya nuna mu a matsayin al'ummar da bata san ciwon kanta ba, bari dai mafi yawan al'amuran da suke jan ragamar rayuwarmu har ma suka tasirantu da zamantakewar mu suna da alaƙa mai ƙarfin gaske da abin da muka yadda dashi ta fuskar addinin mu. Dan haka, yakana da kawaici ba ma'auni bane da zai sanya a auna mutanen yankin Arewa waƴanda mafi yawan su Hausawa ne da munafukai.

 

Matsalolin dake addabar yankin mu ba Gwabnati bace maganinsu, ballantana har a kallemu da munafukai don mun ƙi mu fito zanga -zanga da za ta bayyana mu a matsayin masu yiwa Gwabnati bore.

 

To wai ta yaya ma za muyi bore a gurin da babu maganin matsalar mu?

 

Me zai kaimu asarar lokuntan da ya dace mu yi amfani da su wajen lalubo bakin zaren Matsalolin namu domin nemo hanyar magance su?

 

Yana da kyau mu fahimci cewa, sanin matsalolin mu ya bambanta da sanin dalilan da suka janyo su har ma kuma ya saɓawa hanyar neman mafita.

 

Ta yiwu a baya ina da fahimta irin waccan, kan lamarin yankin Arewa. Amma sakamakon girma na hankali da shekaru gami da na matsayi a dukkan rukunan matakan rayuwata yasa nazari ya faɗaɗa har zuwa gaɓar da sakamakon ya saɓawa bincike da hasashen baya

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State