Ba Zan Taba Yafewa Kishiyar Data Kashe min Yarinya Ba-Mahaifin Da Kishiya Ta Kunnawa Diyyarsa Wuta

Mahaifin da kishiya ta kashe diyyarsa ta hanyar kunnawa amaryar wuta ya bukaci mahukunta da su zartar da hukuncin kisa ga kishiyar' jaridar legit Hausa ta rawaito.

Ibrahim Yayaha Sidi Na Khalifa ya fadi haka ne a zantawar da yayi da gidan jaridar Daily Trust, inda ya ce, Ni abinda da nake bukata shi ne mahukunta su zartar Mata da hukuncin kisa itama.

 

Domin ko a addinin Islama, ma ba laifi ba ne idan mutum da aka zalunta daukar fansa saboda Al-Qur'ani ya fadi cewa hukuncin kisa ba tare da hakki ba.

Don haka "Ba zan taba yafe jinin diyata ba. Qur'an yace ' Mun hukunta cewa rai ga rai'.saboda fadin da Allah yayi ne shiyasa nake son ganin an yanke Mata hukuncin kisa domin wannan abin bakin ciki ne da takaici.

Ki daki yarinya ta har lahira saboda rashin imani kuma ki kunnawa gawarta wuta, saboda wallahi ba zan taba yafewa ba.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author