Babbar Magana: Daga Rakiya Audu Boda Ya Aure Budurwar Abokinsa A Katsina

Da alama dai karin maganar Malam Bahaushe ta cewa Matar Mutum Kabarinsa yayi dai dai, na ganin yadda jarumin wakokin Hausa Audu Boda Katsina ya Aure budurwar abokinsa.

Audu Boda bayan an daura masu ya bayyana cewa, shi fa ko kusa ko alama baida niyyar Aure anan da shekaru 10 masu zuwa, sai gashi kawai ba zato ba tsammani Allah ya kawo karin auren.

Ango Boda ya cigaba da cewa daga raki abokinsa zuwa gidan su Hafsat ne kawai sai reshe ya juye da mujiya, domin da farko ita yarinyar abokina ne ya ce yana son ta.

Domin mu sanannu ne ga Al'umma, toh bayan na raka shi wajenta don suyi hira domin Ni ko layin ma ban taba zuwa ba, shi kenan sai ta leko daga gida ta ganmu sai ta koma cikin gida domin Ni ban ma kula da lekowar ta bah.

“Bayan ta shiga gida ake tambayar ta, ‘Ya ku ka yi da Shi?’ Sai ta kada baki tace da dai Boda ne ya ce ya na son ta…! To, kunji ta yadda mu ka haɗu da ita, kuma Allah ya sa da rabon zan aure ta da kuma taimakon baban ta, don shi abokin yaya na ne.

‘Yan Kannywood da su ka halarta sun haɗa da Abdul D. One, Hassan Danja, Ali Show, M.M. Na Manzon Allah, KB Sikko, Jamil M. Hamid Sakatare da marubuci Nura Salah. Wasu mahalartan sun zo ne daga Jamhuriyar Nijar.  

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author