Babu Wanda Ya Kai Mini Hari A Baga - Gwamna Zulum

 
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta labarin kai masa hari da 'yan ta'adda suka kara kai wa tawagarsa, kamar yadda wasu kafafen yada labarai na gida da kasashen waje suka bayyana.
Malam Isa Gusau, hadimin Zulum na harkar watsa labarai ya sanar a wata takardar sanarwa da aike wa manema labarai a Maiduguri babban birnin Jihar.
A cewar Gusau, Zulum ya je Baga, inda yayi kwana daya yana kula da rabon kayan abinci da sauran kayan tallafi, sannan ya koma Maiduguri ba tare da wani abu ya same shi ba.
"Mun rubuta wannan takardar ne don mu sanar da cewa babu abinda ya samu Zulum ko kuma wani dan tawagarsa, muna musanta labarin da yake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani, wanda yake nuna an kai wa gwamna Zulum farmaki.
"Tabbas gwamnan ya je Baga a ranar Asabar har washegari Lahadi yana garin, don ya kula da raba kayan abinci da kudin tallafi da aka bai wa mutane 5000 mazauna yankin.
Ya samu damar duba gyare-gyare da kuma gine-ginen da gwamnati ta yi a wurin, ba tare da wani abu ya same shi ba.
"Muna son a tabbatar wa da mutane cewa ba gaskiya bane labarin da ake yadawa. Zulum da tawagarsa su na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali," .
"Kamar yadda kowa ya shaida, al'adar Farfesa Zulum ne fadin labarai yadda suke, kuma da a ce an kai masa farmaki, tabbas zai fadi. Babu wani hari da aka kai masa ko tawagarsa, idan wani mai neman labari yana bukatar tabbatarwa, zai iya tuntubar sojojin Najeriya.
"Sannan gwamna Zulum yana mika sakon godiyarsa ga duk masu masa fatan alkhairi, sannan ya jinjina wa jami'an tsaro da 'yan sa kai a kan kokarin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno,".

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author