BAMBANCIN AREWA DA KUDU

Kaga banbancin mutane masu agenda da focus kenan. Attajiri a harkar wakokin Turanci Davido bai damu da yiwa kowane ɗan siyasa waƙa har kawunsa daya fito takarar Gwamna ba. Yana da alaka mai ƙarfi tsakanin sa da Kakakin Majalisa Baban Jamila amma duk ya ajjesu a gefe, yaje da sunan a tattauna abinda ke faruwa tsakanin masu zanga-zangar kawo Karshen SARS da kuma matakan da Gwamnati ta ɗauka. Abin nufi su akan abinda ya shafi lalurorin al'ummar su kawai suke tsayawa kai da fata.

 

Shi kuma Dauda Rarara Attajiri na mawakan Hausa, duk da sanin halin da al'umma suke ciki, amma a hakan sai daya nemi ƙudi a hannun talakawa har jaka biyar, da sunan zai bayyana ayyukan Baba Buhari, tamkar shine Mustafa Boss ɗan masaniyar sanin ayyukan Baba. Babu ruwansa da shigar da kowanne irin koke a gaban wanda yake da ikon gani kai tsaye. Bari kuji, Rarara baida shamaki a fadar Shugaban ƙasa, tun daga kan Tunde, Bashir Ahmad da sauran masu hidima wa Baba Buhari, Rarara yanada damar ganin su kai tsaye kuma suyi masa iso kai tsaye gurin kowane. Haka a gurin Gwabnoni da sauran masu isa a wagga Gwamnatin.

 

Dole muyi haquri a dinga yiwa Arewa nisa a harkokin cigaba na ƙasa. Muna ji muna gani muke rasa alfarmomi da dama saboda jagororin namu ba irin wannan bane a gabansu...

 

Comr Sunusi Mailafiya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State