Bazoum ya lashe zaben shugaban kasar Nijar

Bazoum Mohammed ne ya lashe zaben shugaban kasar ta Nijar da aka gudanar zagaye na biyu, shi ne wanda ya samu kuri'u kashi 55.75 inda abokin karawarsa Mahamane Ousmane ya samu kuri'u kashi 44.25

Issaka Souna shi ne shugaban hukumar zaben wanda ya fadi sakamakon, yace sakamakon zai tabbata ne a lokacin da kotun tsara kundin tsarin mulkin kasar suka tabbatar dashi.

Kafin a ayyana fadin sakamakon zaben, Falke Bacharou shi ne shugaban yakin neman zaben Ousmane wanda yayi zargin cewa zaben an tafka magudi a yayin gunadar da shi, inda Falke Bacharou yayi kira da magoya bayan su dasu fito kan tituna domin bayyana kin amincewarsu da sakamakon zaben.

ECOWAS tana daga cikin manyan kungiyoyin da suka sanya ido kan zaben, inda ta bayyana gamsuwa da yadda zaben ya gudana cikin farin ciki da annashuwa, sai dai wani hadari da aka samu a lokacin da motar jami'an hukumar zabe ta taka wata nakiya a garin Tillaberi,inda aka yi asarar rayukan mutum 7.

 

Sai dai wannan zaben ba karamar nasara ba ce ga kasar Nijar daya daga cikin kasashen Afirka da suka yi suna wajen tafiyar da dimokiradiya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author