BUGA TAKARDUN NAIRA BARKATAI : JAM'IYYAR PDP TA KALUBALANCI SHUGABAN KASA BUHARI.... TANA MAI NEMAN A SAUKE MINISTAN KUDI DAGA MUKAMINTA

AFIRILU 16, 2021

Jamiyyar PDP tayi allawadai da yadda gwabnatin shugaban kasa Buhari suke kokarin karya buga kudaden naira har biliyan 60 Wanda babban bankin kasar ( CBN) yayi .

 

PDP tace yanda babban gwabnan bankin kasar nan (CBN)  Godwin Emefiele , yake buga kudaden naira barkatai ba tare da bin ka'idoji ba a wannan gwabnatin, sun tabbatar da maganar da muke akan gwabnatin APC da shugaban kasa Buhari wajen kwarewa wajen karya cin amana ,yaudara .

 

 

PDP tace ministan Kudi da tsare tsare Hajiya Zainab Ahamed , dayi kokarin yaudarar yan Najeriya ta hanyar karyata zargin da gwabnan Edo ,Godwin Obaseki , inda yace gwabnati ta buga kudaden da suka kai biliyan 60 domin rabawa jahohi a watan Maris .

 

 

Gwabna Obaseki, a matsayinsa na masanin tattalin arziki, Wanda ba dolo bane ,ya zama dole yayi magana idan ya ga ana kokarin yiwa tattalin arziki kanshin mutuwa kamar yadda shugaban kasa Buhari yakeyi.

 

Yanzu ace bazamu iya fito da hanyoyin Samar da kudade ba sai dai ta hanyar ciyowa bashi da buga kudaden ba bisa ka'idaba , wannan ya tabbatar da Buhari bashi da kwarewar daya kamata ya jagoranci kasar nan.

 

Tabbas,a karkashin babban gwabnan CBN "Najeriya muna cikin taskwaro " kuma hakan ya tabbatar da zargin da mukewa gwabnatin Buhari na rusa tattalin arzikin kasar nan.

 

Jamiyyarmu ta damu da yadda ake buga kudaden nan barkatai Wanda hakan yasa naira ta kara faduwa da kashi 18.17 % kamar yadda hukumar kula da kididdigar kudade ta (NBS)  ta tabbatar ranar Alhamis .

 

Wannan kan iya jefamu cikin wani yanayi na rashin tabbas akan tattalin arziki bayan wadda muke ciki yanzu inda miliyiyin mutane basu da abincin da zasuci.

 

PDP tana kira ga shugaban kasa Buhari da ya fito ya fadawa mutane gaskiyar adadin kudaden da CBN suka buga da kuma abubuwan da akayi dasu.

 

Bayan haka, idan ta gaza kare kanta , PDP tana kira da a gaggauta sallamar ministar Kudi ,kuma dole shugaban kasa ya yadda gazawarsace.

 

Jamiyyarmu tana kira ga shugaban kasa Buhari da ya ceci kasar nan ta hanyar bawa kwararru dama musamman a bangaran tattalin arziki tun kafin lokaci ya kure masa .

 

 

Sa hannu:

 

Kola Ologbondiyan

Sakataren watsa labarai

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author