CBN Ya Bayyana Dalilan Da Suka Sa Ya Haramta Hada-Hadar Kudin Zamani Ta Cryptocurrency

Babban Bankin Najeriya CBN, ya bayyana dalilan da su ka sa ya haramta hada-hadar kudin zamani ta’cryptocurrency
Shi dai cryptocurrency ciniki ne wanda Bahaushe ke masa kirari da - :cinikin-biri-a-sama, ko kuma dai a ce ‘kwandala-sayen-mai-kasada’.
CBN ya ce wannan hada-hadar kudade ana amfani da ita ana karkata makudan kudade a duniya kuma ana tura kudade ga masu ayyukan ta’addanci a duniya.
CBN ya kara da cewa sharudda da ka’idojin hada-hadar kudade na 2017 an zartas da cewa an hana tsarin ‘cryptocurrrency’.
Wannan tsari da CBN ya dauka dai ya harzuwa matasa da yawan gaske a cikin kasar nan, musamman ganin cewa Najeriya kasa ta biyu a duniya inda aka fi amfani da tsarin hada-hadar kwandalar zamani, na Bitcoins.
Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Riko na CBN, Osita Nwanisobi, ta bayyana cewa an hana hada-hadar kudi a tsarin ne domin ya na haifar da nakasu sosai a tsarin hada-hadar kudade na game-gari.
“Tsarin hada-hadar kuɗaɗe na kwandala-sayen-mai-kasada, abu ne da ya karya ka’idojin dokokin hada-hadar kuɗaɗe a bankuna wadda Najeriya ta gindaya.
“Tambayar da CBN ke neman amsa ita ce, me ya sa masu hada-hadar za su boye kan su, ba su bayyana a san su ba, idan har abin da su ke aikatawa din daidai ne a bisa ka’idar doka ya ke?”
“Kuma akwai bukatar a fahimci cewa akwai bambanci tsakanin tsarin hada-hadar zamani Digital Currency, wadda wannan tsari ne sahihi wanda babu kumbiya-kumbiya a ciki, to amma shi tsarin ‘cryptocurrency’ abu ne lullube, wanda ba a san wadanda ke yin hada-hadar ba. Kuma ba a san tsakanin wa da wa ake yin hada-hadar ba. Amma kuma su na yi hada-hadar a boye a cikin bankunan kasuwanci.’’
CBN ta damu da tsarin ne saboda ba a san masu gudanar da shi ba, ta yadda ba a iya sa-ido a kan abin da su ke aikatawa da kudin da kuma sahihancin irin hada-hadar da ake yi da kudaden da ake safara a karkashin kwandala-cinikin-mai-kasada’, wato ‘cryptocurrency’.
“Wannan tsari a akwai kumbiya-kumbiya, harkalla karkatar da kudade ana sayen muggan kayayyakin da aka haramta. Kuma ana karkatar da kudade zuwa ga masu ta’addanci ana sayen muggan makamai masu saukin safara.
“Sannan kuma a karkashin wannan tsari, mutane na kauce wa biyan haraji sosai.”
“Tambayar da CBN ke neman amsa ita ce, me ya sa masu hada-hadar za su boye kan su, ba su bayyana a san su ba, idan har abin da su ke aikatawa din daidai ne a bisa ka’idar doka ya ke?”
“Bankuna da yawa da masu zuba jari sun kauce wa tsarin kwandalar cryptocurrency domin kare darajar hada-hadar su. Saboda ana yin amani da tsarin ana aikata muggan laifuka a duniya.” Inji CBN.
Ko yaya kuke kallon wannan matakin na CBN?

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author