China ba itace Kasar da Cutar Corona ta fara aukuwa ba-Inji Wani Masani.

Ba Shakka Dukkanin hujjojin da ke akwai sun nuna cewa kwayar cutar ta corona, wacce ta yiwa mutane fiye da miliyan 56 illa a duniya, mai yiwuwa an fara gano ta ne a garin Wuhan da ke tsakiyar kasar ta China amma ba a nan ta fara akuwa ba, a cewar daya daga cikin manyan masana kimiyya na kasar.

 

 "Wuhan shi ne inda aka fara gano kwayar cutar ta corona amma ba anan ne ta samo asali ba," in ji Zeng Guang, tsohon babban masanin cututtuka na Cibiyar Kula da Rigakafin Cututtuka na China (CDC), yayin ganawa da wani taron ilimi da aka gudanar da ga nesa (online) ranar Alhamis.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author