Cin Hanci Ba Zai Taba Barin Najeriya Ta Cigaba Ba-Ganduje

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa Najeriya ba za ta taɓa cigaba ba sakamakon cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta.
 
Abdullahi Ganduje ya ce babu yadda za a yi Najeriyar nan ta cigaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a kasar.
 
"Za ku yarda da ni idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda ƙasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba," in ji Ganduje.
 
Gwamna Ganduje ya fadi hakan ne a yayin kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas kan wasu dabarun yaƙi da rashawa a jihar.
An kaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis 29 ga watan Aprilun 2021, da nufin rage cin hanci da kuma tabbatar da an gudanar da al'amura a bude a faɗin jihar, a cewar Ganduje wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji.
@Majiya
–BBC Hausa

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author