Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Amince da fara Aiwatar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Nigeria

Da Dumi-Dumi: Buhari Ya Amince da fara Aiwatar Da Shirin Rage Radadin Talauci A Nigeria

 

Kamar Yadda Legit Hausa ta ruwaito, Kwamitin zartarwa na Najeriya, FEC, ya amince da shirin rage radadin talauci da habbaka tattalin arzikin kasa, NPRGS, da kwamitin bawa shugaban kasa shawara, PEAC, ya gabatar.

Cewar majiyar, Femi Adesina, mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan kafafen watsa labarai ne ya bayyana hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a karshen taron mako-mako, a ranar Talata a Abuja.

Ya ce mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, wanda da yake jagorantar PEAC, zai shugabanci kwamiti domin ganin an aiwatar da shirin yadda ya dace.

Adesina ya ce kwamitin na FEC ta kuma amince da aiwatar da shirin cikin tsarin matsakaicin zango da dogon zango na shirin cigaban kasa na 2021-2025 da ajanda 2050.

Har wa yau, kwamitin ta umurci ministan shari'a kuma antoni janar na kasa, Abubakar Malami ya shirya doka da za a gabatarwa majalisar tarayya domin ganin shirin ya dore.

Ku saurari karin bayani…

Source: Legit Hausa

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

GLOBNG HUB - Best for All Globng Hub and SGL is for interested content creators who wants to share their experience to the whole world, you can create account with us, when your account is approve you can then proceed to create contents ranging from entertainment, sports, politics, health and fitness, society news, technology, business and industrial, lifestyle, education, pet and animals etc. The interested thing is you will get paid as far as your contents/articles worth paying. To Register click on the link below https://globng.com/register