DALILAN DA YASA BAZA KA/KI SAMU RANCEN COVID 19 LOAN BA

 

 

 

 

Dalilan da ke iya sa ba za ka/ki samu rancen kuɗin NYIF ko Covid-19 Loan ba

Assalamu alai kum

 

Al’umma da dama na fuskantar tsaiko wurin samun kuɗaɗen da suka nemi rance daga bankin NIRSAL/CBN duk da cewa an amince da kuɗin da za a basu sun sanya lambar asusun da za a tura musu kuɗin.

 

Akwai dalilan da ka iya sawa mutum ba zai samu kuɗin ba kamar haka.

 

1- Karamin ‘account’ wanda baya karban kuɗi me yawa.

 

2 -Samun banbanci tsakanin sunan da kacike fom din rancen Kudi da Kuma sunan dake dauke a account d’in ka.

 

SHAWARA……

 

Duk wanda ya san ya cike Form ɗin neman rancen kuɗin Covid-19 ko NYIF da sauransu to ya tabbatar ya je bankin sa domin ayi gyara masa asusun (Upgrade) saboda gudun samun matsala.

 

Shekarar da ta gabata akwai mutanen da an amince a basu rancen (Approval) amman saboda rashin girman ‘account’ ɗin su hakan yasa har yanzu basu sami kuɗin ba.

 

Sannan ina me baiwa ƴan’uwa shawara duk wanda ya samu kuɗin nan ya tabbatar ya yi abinda ya kamata dasu domin gwamnati ta badasu ne don a yi kasuwanci kuma ka jawo wasu suma suci a ƙarƙashin ka domin rage zaman kashe wando.

 

Fatan za a kiyaye

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author

Blogger