DALILIN DA YASA YAN KUDU SUKE ZANGA ZANGA

DALILAN DA YASA ƳAN KUDU SUKE ZANGA ZANGA.

 

Da farko ban so nayi wannan rubutun a yanzu ba, naso na barshi sai nan da wani lokaci, amma saboda wasu dalilai na yanke shawarar yi, saboda zai fito da wasu abubuwa fili sosai.

 

Wayewar garin jiya Talata na tashi cikin farin ciki da addu'ar alheri ga yankin mu na Arewa dama Nigeria, saboda wasu abubuwan da na samu tabbas akan su, da wanda nake fatan su zama tabbas ɗin.

.

Tattaunawar da nayi da wasu mutane uku akwai abin lura sosai, ɗaya daga cikin su Inyamuri ne kuma ɗan jarida, na waye dashi tun shekaru biyar da suka wuce.

ɗaya kuma Bayarbe ne, ɗaya kuma ba sai na bayyana inda yake ba.

 

Daga cikin abinda Inyamurin nan ya faɗa mun bayan nayi masa tambayoyi, daga cikin tattaunawar mu, sai na jefa masa tambaya kamar da wasa sai ya ban amsa da cewa:

.

A shekara ta 2013 lokacin da aka fara yunƙurin kafa jam'iyyar APC, Bola Tinubu da mutanen sa sun shawarci mutane da dama cewa suna so su haɗa jam'iyya ɗaya da ƴan Arewa, amma suna tsoron munafurcin ƴan Arewa da cin amanar su, an bada shawara wa Tinubu kada ya shiga ƙawancen, amma hasashen abubuwa da dama tasa ya shiga, daga cikin abinda aka faɗa masa shine, wannan Maja da zaka shiga da ƴan Arewa su suna da jam'iyyu biyu ne.

.

Suna da CPC suna da ANPP, kai Tinubu kana da ACN.

Daga Arewa akwai CPC ta shugaba Buhari, ANPP ta Malam Ibrahim Shekarau, sai ACN ta Tinubu.

Aka ce za su fi karfin ka, da wahala su cika maka alƙawuran da suka yi maka, da ace kana da manyan jam'iyyu biyu ne irin na 'yan Arewan toh da zaka iya shiga ba tare da fargaba ba, amma ACN kawai kake da ita.

Shi Inyamurin da muke wannan tattaunawar dashi a waya yace ce:

.

Tinubu ya shiga Maja ne da manyan manufofi guda huɗu, na farko idan an kafa APC ya zamo Vice President ma duk wanda zai zamo shugaba daga Arewa, wannan manufar ta rushe tun a daren da aka yi Primary Election na APC a Lagos, a Teslim Balogun Stadium a 2014.

 

Aka ce ba zai yiwu ba, Buhari shi yaci Primary, Musulmi ne, kaima Tinubu Musulmi, dole dai ka haƙura, amma ka kawo yaron ka guda ɗaya a bashi, dalilin bayyanar Osibanjo kenan a siyasar Nigeria.

.

Na biyu, Tinubu ya shiya Maja ne da nufin ayi masa wasu aiyuka a Lagos, musamman Titin Lagos zuwa Ibadan, da jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Lagos, yayi nasara anyi masa wannan.

 

Manufar sa ta uku itace ya samu kashi 40 na muƙaman gwamnatin da APC ta kafa, itama wannan manufar bata samu karɓuwa ba, domin Buhari yayi jifa da ita, inda ya tattare manyan muƙaman ya miƙa wa mutanen ku na Arewa (inji Inyamurin)

.

Sai manufar sa ta huɗu na shiga Maja:

Idan Buhari zai yi shekaru huɗu ne, toh shi zai gaje shi, shi zai karɓa daga 2019, idan kuma Buhari ze yi Takwas ne toh zai haƙura aje 2023 sai ya karɓa (shi Tinubu).

 

Wannan manufar tasa itace mafi girma, da ita yake kwana da ita yake tashi.

Kuma wa ita ya ajiye ma kudi, Kuma yake kan ajiyewa.

.

Sai dai yanzu haka ya samu tabbas wannan manufar tasa an rushe ta cikin hikima da dabara, babu ita indai ta hannun Buhari ne, Tinubu "ya gama samun tabbas anci amanar sa" (kalmar da Inyamurin yayi amfani da ita kenan).

 

Duk hanyar da yake ganin zai bi ta dan ya zamo shugaban ƙasa an rufe ta, an toshe masa, misali:

Last hope ɗin Tinubu a APC shine Adams Oshiomole, an kwace APC a hannun sa da ƙarfi, ta hanyar amfani da kotu.

.

Na biyu shugaban ƙasa ya rage ƙarfin Osibanjo da kashi 60, ta hanyar janye Advisers ɗin sa, da ƙwace wasu aiyukan da ada Osibanjo ne ke yi, kamar Social Investments programs, da aka karɓe aka mayar dashi Ministry of humanitarian, na Hajiya Sadiya Umar Faruq.

 

Na uku, an ƙwace Ministry of Power daga hannun yaron Tinubu, wato Fashola, an baiwa ɗan Arewa Saleh Mamman, shi Fashola an barshi da Gidaje.

 

Me yasa ka daina jin motsin Osibanjo, baka ganin sa ma ko a hotuna, me yasa ka daina ganin Fashola yana Ziyarar aiyuka da ya saba yi a baya?

.

Waɗannan da ma wasu suna daga cikin dalilan zanga zangar #ENDSARS, wanda mu ƴan ƙabilar Igbo babu ruwan mu, sai yanzu da yaga anci amanar sa a APC sannan zai zo ya tayar da rikici, ada bai san damu ba, dan haka ba ruwan mu.

 

Shiyasa kaga zanga zangar tafi yawa a Lagos, Yarbawa ke yin ta.

Gidan Radio da suka buɗe da Yarbanci suka buɗe shi.

 

Dan haka babu wani Inyamurin da zai yarda ya shiga wannan rikicin.

(Dan Arewa kaji, inyamuri ma ba zai shiga ba balle kai da ake so a ƙwace daga hannun naka).

.

Daga ƙarshe nace toh kana ganin waye Buhari yake so ya gaje shi daga arewa APC, yace mun ina zaton wani mutum ne daga jihar  (Bauchi), bai faɗi sunan sa ba, amma kowa zai gane (Alhaji Ahmad Adamu Mu'azu) ne, daga North East yake.

 

Yana daga cikin dalilan da suka sa Buhari ya dage aka mika shugabancin APC wa wani gwamna daga North East ɗin, Mai Mala Buni.

Saboda akwai abinda ake so a cimma.

.

Wani zai ce yaya za'a yi Buhari ya kammala mulki daga Arewa, kuma wani ɗan Arewa ya gaje shi, a jam'iyya ɗaya? wasu daga cikin masu son ayi dai daito wurin mulkin karɓa karɓa a ƙasar nan suna ganin Buhari zai jawo rikici idan ya dage lallai sai ɗan Arewa ya gaje shi.

 

Zan tsaya da rubutun a nan haka, idan lokaci ya samu nan gaba insha Allahu zan bayyana wasu abubuwan da zasu haske maka wasu lamuran.

.

Amma yanzu Kam ka sani wannan zanga zangar lamarin neman mulki ne kawai ya jawo ta, wani ko wasu suna ganin zasu yi asaran jarin da suka zuba a kasuwar siyasa.

Allah ya kyauta, ya tare mu.

 

  1. Allah ya taimaki Baba, ya tsare shi, ya inganta masa manufar sa mai kyau akan mu.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author

I'am Muazu Muhammad from Gwandu Local Government Kebbi State