Dan Najeriya ya jagoranci samar da rigakafin Cutar Korona a Amurka.

Cutar korona na daya da cikin cutukan da ta addabi Duniya kuma tayi sanadiyar hallaka mutane da dama inda har ila yau ake ta kokari wajen samar da magani ko Rigakafin ta.

Gidan Rediyon BBC ya ruwaito cewa

 "Rigakafin korona da kamfanin Pfizer ya samar an bayyana cewa ɗan asalin Najeriya ne ya jagoranci samar da rigakafin a Amurka.

 

Ofishin jekadancin Amurka a Najeriya ya wallafa hoton likitan Dr Onyema Ogbuagbo a Twitter tare da cewa shi ya jagoranci samar da rigakafin korona na farko mai inganci a Amurka.

 

Onyema Farfesan magani ne da cuttuka masu yaɗuwa a Jami'ar Yale.

 

Ya yi digirinsa na farko a Jami'ar Calabar 2003".

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author