Dole Real Madrid Ta Kashe Kudi A Kasuwar ‘Yan Wasa Mai Zuwa –Roberto Carlos

Tsohon dan wasan Real Madrid, Roberto Carlos yace, wajibi ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ta fitar da makudan kudade domin sayo manyan zaratan ‘yan wasan da zasu sake d'aga kungiyar daga cikin jerin manyan kungiyoyi a duniya anan gaba saboda kungiyar yanzu tana bukatar canji sosai.

Carlos ya shaida haka ne bayan da aka tashi wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kungiyar kwallon kafa ta Huesca a gasar cin kofin La liga na kasar Andulus (Spain) a ranar Asabar inda dan wasan baya na Madrid Raphael Barane ya ci wa Real Madrid kwallo biyu, inda ta sami nasarar doke Huesca da ta ke kasan teburin na  La Liga a wasan mako na 22.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author