Duk Wanda Ya Rubuta Labarin Cewar Ina Neman Miji Aure Ya Cuceni, Saƙon Ummi Zeezee Ga Ƴan Najeriya

"Salam to Nigerians. Duk wanda ya rubuta wannan labarin na cewar ina neman mijin aure to ya cuce ni don yanzu ya sa ko wanne TOM AND JERRY sai ya dinga aiko min da hoton sa ta WhatsApp line ɗi na wai zai aure ni, an hana ni sakat."
 
"Ba hali in hau online na dinga ganin text messages masu uban yawa wanda ban isa in iya karanta duka wasiƙun ba da hotunan maza su ma da yawa kala-kala."
 
"To dan girman Allah duk wanda ya min wannan tsiyar na cewa ina neman mijin aure ya san kan sa ko ni ban sanshi ba saboda haka ka dubi darajan Annabi da Alƙur'ani kada ka sake min ƙarya irin wannan domin maza su na damu na sosai yanzu bayan kuma ina da saurayi na da na ke so shi ma ya ke so na! Haba, mtswwww!" Inji Zeezee

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author