Fama Da Ciwo A Tushen Babban Yatsan Hannu Ne Matsalar Dake Damun Ku?

Ciwon "De Quervain's Tenosynovitis" yana faruwa ne sakamakon kumburar jijiyon tantani da suke sadar da tsoka ga zuwa ƙashi. Waɗannan jijiyoyin tantani guda biyu sune suka sadar da tsokokin da suke ɗaga babban yatsan hannu sama.
 
 
A lokacin da waɗannan jijiyoyi suka kumbura suna samun wahalar zirga-zirgar da suke yi yayin lanƙwashewa da miƙar da babban yatsan hannu.
Ayyukan da ke buƙatar maimaituwar motsin yatsu hannu akai-akai na daga cikin ayyukan da ke haddasa wannan ciwon.
Misalan ayyuka ko sana'o'in sun haɗa da rubuce-rubuce ✍🏻, zane-zane, goge-goge tsawon lokaci da duk aikin da ke buƙatar maimaituwar aikin babban yatsan hannu.
Da zarar ka fara fuskantar alamun wannan ciwo tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai.
 
 


 

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author