Garkuwa Da Mutane: An Sako Budurwar Da Aka Dauke A Garin Birnin Kebbi

Masu garkuwa da mutane sun sako budurwar nan Naja'atu wadda suka yi garkuwa da ita a unguwar gangaren NEPA dake yankin tudun Wada a cikin garin birnin kebbi.
 
Majiyar mu ta sami labarin cewa mahaifin budurwar ya shaida wa manema labarai cewa 'Yar tasa tana cikin koshin lafiya.
 
Sai dai wata majiyar ta shaida cewa an biya kudin fansa kafin sako budurwar, ya zuwa yanzu dai ba'a bayyana ko adadin nawa aka bayar ba domin karbo budurwar.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author