GBAJABIAMIALA YA ZIYARCI IYALIN MAI SAYAR DA JARIDAR DA DAN SANDAN SA YA BINDIGE

 
*Kakakin majalsar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamiala ya ziyarci iyalin mai sayar da jarida Ifeanyi Okereke a Suleja jihar Neja; wanda dan sanda a tawagar sa ya bindige har lahira. Lamarin ya auku ne ranar alhamis lokacin da Gbajabiamiala ya fito daga majalisar inda ya tsaya wajen masu sayar da jarida kamar yanda ya saba don gaisawa da su amma daga bisani sai dan sanda a tawagar ya bude wuta da ya sa albarushi ya doki kan Okereke ya yi sanadiyyar mutuwar sa.
 
*Kakakin ya kare akasin da cewa tun da dadewa dama ya kan tsaya don gaisawa da masu sayar da jaridar da ya ce mutanen sa ne, amma yayin da zo barin wajen sai wasu su ka nemi birkita tafiyar kwambar motocin da ya sanya jami'an sa bude wuta a cikin iska da ya sa harsashi ya yi batan kai ya hallaka Okereke. Gbajabiamiala wanda a ke cewa mai matukar girman kai ne don ba ya amsa gaisuwar mutane ta haka kawai, ya musanta lamarin da cewa ya na girmama mutane ba tare da la'akari da matsayin su ko arzikin su ba.
*Kakakin ya ce ya bude wani asusu don kula da 'ya'yan marigayin ciki har da jinjiri da ba a yi sunan sa ba, har sai sun kai shekaru 21. Gbajabiamiala ya gaiyaci masu sayar da jarida su zo zauren majalisar a talatar nan don za a karrama marigayin.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author