Gina Gidan Gwamnati Irin Na Zamani Babagana Zulum Ne Ya Fara Aza Harsashi A Jihar Bauchi

A safiyar yau ranar Alhamis 04 ga watan, Maris 2021, mai girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed tare da takwarorinsa na shiyyar Arewa Maso Gabas suka halarci bikin sake ginawa da daga darajar gidan Gwamnatin Bauchi Domin ya zamo an inganta shi yanda zai dace da zamani.
Maigirma Gwamnan yace aikin ya zamo wajibi ne domin tun zamanin mulkin soji aka gina gidan Gwamnatin wanda akwai bukatar sake fasalin sa a halin yanzu .
 
Ya ce aikin zai mai da gidan Gwamnatin jihar mai inganci sosai yanda za'a samu shashi-sashi da kuma babban dakin taro na Duniya . Da Ofisoshin ma'aikata, inganta Asibiti da kuma masallaci. yanda Za'ayi hanya da inganta hanyar samar da ruwa sha
Yanda gidan Gwamnatin zai dace da wannan zamanin.
Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas. Wanda ya jagoranci aza harsashin sake gini da inganta gidan Gwamnatin jihar Bauchi.Ya yaba ma kokarin Gwamnan jihar Bauchi na kawo cigaba ma jihar wanda yace Gwamna Bala Muhammad yana kokarin sabunta jihar Bauchi ne a halin yanzu .
Zulum yace_:fatan mu shine Arewa maso gabas ta haska ta daukaka baki daya.
A karshe Gwamna Umara Babagana Zulum. Ya mika Godiyar sa ga Gwamnati da jama'ar jihar Bauchi kan irin tarbar da suka yi musu a yayin taron Gwamnonin yankin arewa maso gabas da karo na 4 da sukayi a jihar Bauchi.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author