Guardiola: Shin Ko Gwarzon Dan wasan Bercelona Lionel Messi Zai bar kulof dinsa?.

Mai horar da yan wasa a club ɗin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ya fi son Lionel Messi ya kammala rayuwarsa ta ƙwallon kafa a Barcelona.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa:

 

"Guardiola ya tsawaita kwangilarsa da Manchester City inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a ranar Alhamis, kuma nan take aka alaƙanta da shi da tsohon ɗan wasansa wanda saura kaɗan ya dawo ƙarƙashinsa.

 

A ƙarshen bazara kwangilar Messi za ta kawo ƙarshe kuma yana iya ƙulla yarjejeniyar da duk wata ƙungiya a wajen Spain daga watan Janairu".

 

Guardiola ya ce: " Messi ɗan wasan Barcelona ne. Na fada ba sau ɗaya ba. a matsayi na masoyi, ina son Leo ya ƙare rayuwarsa a can"

 

A watan Agusta Messi ya so barin Barcelona, kuma lokacin an yi tunanin zai koma Man City kafin shugaban Barcelona ya hana shi tafiya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

About Author