Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa ‘Yan Kasuwar Da Suka Yi Gobara A Sakkwato Da Miliyan 30

Gwamnan Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya tallafa wa ‘yan kasuwar jihar Sakkwato da suka yi mummunar gobara a ranar 19 ga watan Janairun, shekara 2021.

Da sanyin safiyar ne, Sanata Abubakar Bagudu ya tallafawa 'Yan kasuwar da naira miliyan 30, Inda gobarar tafaru a babbar kasuwar garin Sakkwato sai dai gobarar lashe makudan kayayyakin dukiya masu tarin yawa.

Rahoton hakan na dauke ne cikin wata takarda mai sa hannun Muhammad Bello babban mai bayawa Gwamna Tambuwal shawara ga harkokin yada labarai.

Gwamnan jihar kebbi Sanata Atiku Bagudu, ne cikin manyan mutane da suka fara kai ziyarar  a wannan kasuwa domin jajantawa ‘yan kasuwa da gwamnatin Jihar ta Sakkwato jajen abin daya afku dasu.

Gwamnan yace ziyarar da ya kawo wa Gwamnan Jihar ta Sakkwato Hon: Aminu Waziri Tambuwal ya zo ne domin jajantawa Gwamnati da kuma jama’ar Jihar Sakkwato, ya kara fadin cewa dukkan abin da ya shafi Jihar Sakkwato kamar ya shafi jihar sa ne.

Gwamnan jihar Sakkwato Hon: Aminu Waziri Tambuwal da yake mayar da jawabi shima yayi godiya ne tare da fadin cewa wannan tallafi da Gwamna Bagudu ya bayar alama ce da take nuni cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninsu da kuma ‘yan uwantaka da ke tsakanin Jihohin biyu Sakkwato da Kebbi.

Hon: Aminu Waziri Tambuwal ya cigaba da fadin cewa babu wani rai da aka samu labarin an rasa shi sakamakon barkewar gobarar, Gwamna Tambuwal ya tabbatar da cewa jami’an hukumar kashe Gobara da suka hada da na Gwamnatin Jihar Sakkwato da Gwamnatin tarayya da kuma na babban filin Jirgin saman kasa da kasa Sultan Abubakar na uku, duk sun kawo babbar gudunmawa gurin aikin dakile gobarar.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author