Gwamnatin Tarayya Taba Jihar Borno Biliyan Uku Don Ginawa 'Yan Gudun Hijira Gidaje

Gwamnatin Najeriya ta bayar da kudaden da yawansu ya kai kimanin naira Biliyan uku domin gina kashin farko na gidaje dubu 10 da za'a sake mayar da 'yan gudun hijira a jihar Borno.

Gwamnan jihar Borno  Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ziyarar gani da ido da ya kai a sashen da za'a gina sabbin gidajen na garin Dalori dake karamar hukumar Konduga dake jihar Borno.

Gwamna Zulum yace,gwamnatin ta bayar da kudaden ne ga jihar domin tabbatar da aiwatar da wannan muhimmin aiki domin 'yan gudun hijirar su dawo gidajen su, su cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba a shekarun baya.

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author