Haukar Abduljabar Bata Kai Ace Baza A Zauna Dashi Ba-Sheikh Bello Yabo

Sheikh Muhammad Bello Yabo Malami ne mai wa'azin addinin Islama a Najeriya, ya bayyana cewa idan Malam Abduljabar yana da hauka to haukar sa bata kai cewa baza a zauna da shi ba, domin mu agun mu Malami ne.

Malam Bello Yabo yace matukar ana so a zauna lafiya a garin Kano, toh a zauna da Abduljabar domin ya ci mutuncin Manzon Allah kuma duk wanda ya ta6a mutuncin Manzon Allah ba'a hukunta shi ba, wai harma abar shi yana yawo a gari toh ko shakka babu kamar fada ake nema agun Al'umma.

"Saboda haka dole ne a zauna da Abduljabar domin a tuhume shi saboda tun kafin ya karanta Littattafan da yace a ciki yaga anci mutuncin Manzon Allah muka karanta shi" inji Malam Bello Yabo.

Shehin Malamin ya cigaba da cewa yin hakane zai kwantar da hankulan Al'ummar Musulmi, duk da yace Wasu Malamai daga cikin Ahalul-Sunnah suna cewa ba sai an zauna da shi ba to fahimta ce, Fahimta kuma gaskiya ce, amma mu muna goyon bayan a zauna dashi.

Kun iya ziyartar Link din da ke kasa domin kallo hirar kai tsaye.

https://www.facebook.com/alahbabtv/videos/277659177261804/

Enjoyed this article? Stay informed by joining our newsletter!

Comments

You must be logged in to post a comment.

Related Articles
About Author